Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun tabbatar da kisan wani hakimi da ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Maru.
Wata sanarwa da kakakin rundunar SP Muhammad Shehu ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen Kujemi da ke gundumar Ɗansadau
Kakakin Rundunar ya ce ƴan bindigar sun dirarwa ƙauyen ne inda suka kashe hakimin garin da kuma wani Mustapha Halilu.
