Home Labarai ‘Yan bindiga sun kashe limami a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe limami a Kaduna

459
0

Wasu ’yan bindiga sun hari kauyen Kawaran Rafi da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, inda suka kashe babban Limamin garin, Dan Liman Isah.

Majiyar DCL Hausa ta samu labarin cewa maharan sun tarar da marigayin har inda suka harbe shi nan take bai ko shura ba kuma suka kama gabansu ba tare da dibar wata dukiya ko satar wasu mutane ba.

Ana ganin cewa kisan gillar da aka yi wa malamin na da nasaba ne da da’awarsa ta bayyana tsagwaran adawa a kan yadda ’yan bindiga ke famar cin karensu babu babbaka wajen aikata ta’addanci na kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply