Kimanin mutum 19 ne aka kashe a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Kukum Daji da ke karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kai harin ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Lahadi.
Rahotanni sun kuma nuna cewa mutum 30 da suka tsallake rijiya da baya sun samu raunika daban-daban.
Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Mr. Yashen Titus, ya shaidawa ‘yan jarida a ranar Litinin cewa ‘yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokaci da kuma bayan wani daurin aure da aka gudanar a kauyen.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da harin, saidai ya ce ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutun ba.
