‘Yan bindiga sun kama Kabir Lawal Goma a kwanaki ukun da suka gabata a jihar Kaduna inda suka bukaci a ba su kudin fansa Naira milyan biyu wadda kuma danginsa sun kai musu amma kuma duk da haka sai da suka kashe shi kamar yadda wani abokinsa ya tabbatarwa jaridar DCL Hausa.
Kafin kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi masa Kabir Lawal Goma ya kasance matashi mai sana’ar sayar da kashin kaji a garinsu Jargaba da ke Karamar Hukumar Bakori ta jihar Katsina. Kuma masu garkuwa da mutanen sun kama shi ne a sa’ilin da yaje Kaduna don ya saro kashin kajin don ya zo ya sayar wa manoman yankinsu.
Ya mutu ya bar ya bar yara uku da mata daya.
