Home Labarai ‘Yan Bindiga sun kashi Hakimi, Dan Uwan sa, wasu 9 a Kaduna

‘Yan Bindiga sun kashi Hakimi, Dan Uwan sa, wasu 9 a Kaduna

93
0

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai kashe mutum 11 ciki har da wani basarake a kauyuka uku da ke jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar jama’ar kudancin Kaduna Mr. Luka Biniyat ya fitar da yammacin jiya Talata, ya ce an kai harin ne a kauyukan Guruku, Kuduru, a karamar hukumar Chikun, da kuma Jagindi a karamar hukumar Jema’a.

Ya ce an kashe mutune 6 a kauyan Guruku, bayan ‘yan bindigar sun kai hari a garin da yammacin jiya Talatar.

A cewar sa, a ranar Litinin ne maharani suka ka yi dirar mikiya a gidan Hakimin Jagindi Danlami Barded a misalin karfe 8 na dare, inda suka kashe shi tare da dan uwan sa.

Rahotani sunn nuna cewa an kashe marigayan ne, a lokacin da suke sasanta wanni rikicin cikin gida a tsakannin su.

Haka ma shugaban karamar hukumar Jema’a Peter Averik, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni jami’an tsaro suka ziyarci inda abun ya faru.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply