Home Labarai ‘Yan bindiga sun kona mutum 16 ‘yan gida daya kurmus a Kaduna

‘Yan bindiga sun kona mutum 16 ‘yan gida daya kurmus a Kaduna

60
0

Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari a kauyen Bakali da ke gundumar Fatika a karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, sun kone iyalan wani gida su 16 kurmus.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari a kauyen ne da misalin karfe 4 na yammacin jiya Talata inda suka banka wuta tare da kone rumbunan hatsi, motoci da Babura da dama.

An ce ‘yan bindigar sun kulle mutanen 16 ne a cikin daki sannan suka bankawa gidan wuta.

Wani mazaunin garin da ya tabbatar da faruwar lamarin Alhaji Sani Bakali ya ce sama da ‘yan bidiga 100 ne saka dirarwa garin.

Zuwa lokacin hada wannan labara dai, rundunar ‘yan sandan jihar bata ce uffan ba kan batun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply