Wasu da ba a san ko su wanene ba sun sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa Philip Shekwor.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bola Longe da ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yanjarida a birnin Lafiya, ya ce mutanen sun ziyarci gidan shugaban jam’iyyar da misalin karfe 11 na daren Asabar suka yi awon-gaba da shi.
Ya ce har yanzu dai ba a san inda mutumin ya ke, amma dai jami’an tsaro na bakin kokarinsu domin ganin an ceto shi cikin aminci.
