Home Labarai ‘Yan bindiga sun sake kai hare-hare a Sakkwato

‘Yan bindiga sun sake kai hare-hare a Sakkwato

204
0

Da almurun Talata ne ‘yan bindiga suka afka ma wasu kauyukka cikin karamar hukumar Issa da ke gabashin Sakkwato inda suka kaddamar da hare-hare a garuruwan Bafarawa, Kamarawa Sududdu6u, garin Fadama, da kuma garin Arume.

Tun dai da misalin magariba ‘yan bindigar ke cin karen su har tsakkiyyar dare a wadannan kauyuka, inda suke shiga gida-gida.

Wasu mata da maza da DCL Hausa ta zanta da su sun ce sun kashe mutum biyu, sannan sun tattara dabbobi da dukiyoyin su, sannan sun 6a66ala shaguna sun kwashe kaya sun yi awon gaba dasu kaf.

Yanzu haka Mata da maza da yara suna bakin wani kogi don isa garin Issa da ke zama hedikwatar karamar hukumar.

Matan sun ce ba su yi barci ba a daren Talata, ga yunwa su na ji, kananan yara kuka kawai suke yi.

Sun ce kusan kullum sai sun shigo yankunan nasu duk da cewar suna jin karar jiragen soji na shawagi a sararin samaniya, amma hakan bai hana su gudanar da ta’asar su.

Yanzu haka mutanen wannan yanki duk sun watse sun tarwatse suna ta neman inda zasu 6uya da rayuwar su.

Koda a ‘yan kwanakin nan jiragen yaki na soji kusan takwas aka kai a jihar Sakkwato don yakar wadannan ‘yan ta’adda amma har ya zuwa yanzu suna cin karen su babu babbaka.

DCL Hausa ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ASP Muhammad Sadiq Abubakar yace zai kira daga baya, amma zuwa lokacin rubuta wannan rahoton shiru ba wani labari daga gare shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply