Home Sabon Labari Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a jihar Sokoto

Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa a jihar Sokoto

88
0

A daren Litinin ne rahotanni suka ambato wasu masu dauke da makamai sun kai hari a kauyen Sabaru cikin karamar hukumar Dange shuni ta jihar Sakkwato inda sukayi garkuwa da wani attajiri Alhaji Tukur Sabaru.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin ta ASP Muhammad Sadiq Abubakar.

Ko da ya ke yayin artabun sun harbi wasu mata biyu da harsasai wadanda yanzu haka matan su na karbar magani a asibiti.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Sokoto ta bayyana cewa tana iyakar yin ta na magance matsalar rashin tsaro a jihar. Ya zuwa yanzu dai lamarin rashin tsaro na kara tabarbarewa a jihar Sakkwato. Mahukumtan jihar kuma na ci gaba da daukar matakan tsare rayuwar jama’a.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply