Home Sabon Labari ‘Yan China sun yi yunkurin ba EFCC cin hanci

‘Yan China sun yi yunkurin ba EFCC cin hanci

254
0

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta ce ta kama ‘yan kasar China biyu bisa zargin yunkurin bai wa jami’inta cin hanci.

A taron manema labarai da Shugaban Yankin Sokoto na Hukumar  Abdullahi Lawal ya kira ya ce jami’ansu sun kama Mista Meng Wei Kun da Mista Xu Koi a unguwar Kasarwa a Sokoto bisa zargin bai wa shugaban EFCCC reshen yankin Sokoto Abdullahi Lawal, cin hancin miliyan 50 a cikin yarjejeniyar da suka yi za su ba shi miliyan 100 toshiyar baki.

A cewar EFCC, mutanen biyu sun bayar da cin hancin ne domin su hana binciken da ake gudanarwa kan kamfanin gine-gine na China Zhonghao Nig. Ltd, wanda gwamnatin jihar Zamfara ta bai wa kwangilar da ta kai Naira biliyan 55 tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

Hotan ‘yan kasar Chinan da ake zargin sun yi yunkurin bayar da cin hanci a Sokoto

Shugaban hukumar reshen jihar Sokoto yana binciken kamfanin ne game da aiwatar da kwangilolin gina hanyoyi a garuruwan jihar Zamfara da haƙa rijiyoyi 168 masu amfani da hasken rana a kananan hukumomi 14.

EFCC ta ce ‘yan kasar ta China sun razana ne saboda yadda suka ga shugaban hukumar reshen jihar ta Sokoto yana gudanar da aikinsa ba sani ba saboda, abin da ya sa suka nemi ba shi cin hancin miliyan 100.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply