Home Labarai ‘Yan fansho sun koka kan rashin biyan su hakkokinsu

‘Yan fansho sun koka kan rashin biyan su hakkokinsu

119
0

Shugabannin ‘yan fansho da sauran mambobin su a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun koka tare da nuna damuwa dangane da yadda gwamnatocin jihohi ke yin biris, su hana su hakkkokinsu.

Shugaban ‘yan fansho na yankin arewa maso yamma Alh sani Mohd Gobirawa a wata ganawa da DCL Hausa, yana nuna takaicin sa kan yadda mafi akasarin jihohin arewa maso yamma ba su fi jiha 3 kacal ba da ke sauke hakkkokin ‘yan fansho tsakani da Allah.

Alh sani Mohd Gobirawa ya nuna irin yadda suka shiga wani halin ni ‘yasu sakamakon rashin kula da daawainiyar Iyalan su, amma kuma gwamnatoci sun hana masu hakkkokinsu.

Bugu da kari, ‘yan fanshon sun koka kan yadda aka kasa saka su cikin mafi karancin albashi na dubu goma Sha takwas, balantana uwa uba na naira dubu talatin, wannan ya sa su kira da gwamanti ta yi wa Allah ta dubi halin da suke ciki da kuma makomar iyalan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply