Home Labarai ‘Yan fansho sun toshe kofar shiga gidan gwamnatin Gombe

‘Yan fansho sun toshe kofar shiga gidan gwamnatin Gombe

22
0

’Yan fansho a jihar Gombe sun gudanar da zanga-zangar lumana kan rashin biyansu kudaden fansho da na garatuti na wata-wata.

Tsoffin ma’aikatan sun yi dandazo inda suka toshe babbar kofar shiga gidan gwamnatin jihar, suna masu shan alwashin sai sun gabatar da takardar korafi ga Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.

Shugaban kungiyar ‘yan fansho ta Nijeriya (NUP), Muhammad Abubakar ne wanda ya jagoranci masu ‘yan fanshon jihar, ya yin zanga-zangar lumana, mambobinsu kungiyar na bin gwamnatin jihar basussuka na sama da shekaru tara bayan sun yi ritaya daga aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply