Home Sabon Labari Yan fansho za su fara zanga-zanga a jihar Benuwai

Yan fansho za su fara zanga-zanga a jihar Benuwai

71
0

Saleem Ashiru Mahuta/dkura

 

Yan fansho a jihar Benue da ke Tsakiyar Nijeriya sun yi kurarin hana duk wasu aikace aikacen gwamnati a jihar har sai an biya su kudaden su wanda suke bin gwamnatin jihar.

Jaridar Independent ta bayyana cewa duk da ba ta gano yawan kudin da yan fanshon ke bin gwamnatin ba, wasu daga cikin ma’aikata sun tabbatar da cewar yan fanshon  jihar da kuma na kananan hukumomin jihar na bin  sama da Naira biliyan 25.

Sun bayyana matsayarsu a cikin wata takarda da suka tura ga gwamnan jihar Samuel Orton, wanda kuma aka aike ta ga manema labarai a Makurdi a jiya Lahadi, inda yan fanshon suka bayyana wa gwamnan sun shirya gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin jindadin su kan kudaden da suke bin gwamnatin na tsawon watanni 25.

Sai dai duk wani yunkuri domin jin ta bakin Sakataren yada labaran gwamnan Terver Akase da kuma kwamishinan yada labarai Ngunan Addingi ya ci tura inda suka yi ta bayayya akan wanda zai yi magana akan batun.

Sai dai a cikin takardar da shugaban kungiyar Peter Kyado da mataimakin sakatare James Mac-Mtsor suka sanya wa hannu, sun jawo hankalin gwamnan kan wasu takardu biyu da suka aike masa akan batun inda suka ce sun nemi a sasanta abin cikin ruwan sanyi amman hakan ta gagara, wanda a cewar su sun yanke hukuncin fara zanga-zanga a duk fadin jihar har sai an biya su kudadensu wanda kuma za su fara daga ranar Laraba 4 ga watan Satumban da muke ciki

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply