Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi ‘Yan kasuwar Nijeriya a Ghana sun yi zanga-zanga a Abuja

‘Yan kasuwar Nijeriya a Ghana sun yi zanga-zanga a Abuja

125
0

‘Yan kasuwar Nijeriya da ke Ghana sun yi zanga-zanga zuwa ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya da ke Abuja don nuna rashin jin dadinsu kan rufe masu shaguna a kasar Ghana.

Masu zanga-zangar, wadanda ke dauke da kwalaye dauke da rubutu daban-daban da ke nuna bacin ran nasu, sun gudanar da zanga-zangar a ranar Laraba, cikin lumana karkashin kulawar jami’an ‘yan sanda.

Shugaban masu zanga-zanagar Nze Ugo-Akpe Onwuka, ya ce hakurinsu ya fara karewa, domin kuwa tsawon shekara bakwai kenan suna jiran gwamnatin Nijeriya ta shiga batun, amma ba abun da ya faru.

Ya ce halin da ‘yan kasuwar Nijeriya ke ciki a kasar Ghana ya kai inda ya kai, kuma idan ba a dauki mataki ba, ‘yan kasuwar za su rika fuskantar hare-haren nuna kyama.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply