Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi ‘Yan kurkura za su rika biyan haraji ta banki a Kano

‘Yan kurkura za su rika biyan haraji ta banki a Kano

29
0

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da matuka babur adaidaita sahu za su biya haraji N100 a kullum amma za a je banki ne a biya, ta hanyar #Remita, wadda duk lokacin da aka je biyan kudin, za a biya kudin Remita #600.

Ma’ana kowanne direban Dan-sahu zai kashe akalla #700 a kullum wajen biyan kudin harajin, idan ka lissafa a shekara zaka samu akalla #255,500.

Saboda a ragewa mutane wahalar zurga-zurgar da bata lokaci wajen biyan kudin, sai gwamnati tace, za su iya biyan kudin kamar haka:

Wata daya #3,000
Wata uku #9,000
Wata shida #18,000
Wata Tara # 27,000
Shekara #36,000

Duk da haka saboda gwamnati naso ta karfafa musu gwiwar biyan kudin, sai tace ta yi rangwamen kaso 25% ga duk wadda zai biya, kudin wata shida, tara, da shekara daya.

Wadda zai biya kudin shekara #36,000 kudinsa zai koma #27,000, kudin wata Tara #27,000 zai koma #20,250, shima mai biyan kudin rabin shekara #18,000 zai koma #13,500.

DCL Hausa ta samu labarin cewa bayan gwamnati ta zauna, da shugabannin kungiyoyin Yan Adaidaita sahu, ta fada musu tsare-tsarenta game da biyan kudin harajin, da kuma lokacin da za’a fara kamen wadanda basu biya kudin harajin ba, sai suka roki gwabnati da ta kara musu, Kuma gwabnati ta aminta ta Kara musu sati biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply