Shugabannin majalisar wakilai ta Nijeriya na ganawar sirri yanzu haka da shugabannin tsaro na kasar a Abuja.
Mataimakin shugaban majalisar wakilai Ahmad Wase ne ke jagorantar ganawar sirrin da ta fara da misalin karfe 2:15 na rana.
An dai fitar da ‘yanjarida da sauran wadanda lamarin bai shafe su ba waje a daidai lokacin da za a fara gudanar da ganawar.
Daga cikin wadanda suka halarci taron ha da jami’ai daga hedikwatar tsaro ta kasa, rundunar sojin sama, ta sojin ruwa, ‘yansanda, jami’an kula da shige da fice, na farar hula, da jami’an kula da gidajen yari da dai sauransu.
