Biyo bayan karin kudin wutar lantarki da farashin litar man fetur, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya tsoron Allah wajen tafiyar da akalar mulkin kasar nan.
Secodus wanda ya bayyana haka a ya yin taron da jam’iyyar PDP a Abuja, ya tunasar da jam’iyya mai mulki ta APC cewa ba a zabe ta don azabtar da ‘yan Najeriya ba.
ya kuma yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kasance mai tawali’u tare da sanya tsoron Allah a koda yaushe wajen gudanar da al’amuran da suka shafi Nijeriya.
