Hukumar dakile yaduwar cutuka ta Nijeriya NCDC ta ce an samu karin mutane 386 da suka kamu da cutar corona a kasar a sakamakon ranar Asabar 01.08.2020.
Ta ce an yi wa mutane dubu 300 gwajin cutar ya zuwa yanzu a kasar.
Jihar Legas ce ke kan gaba sai Abuja da Oyo ta biyu da ta uku, a ya yin da jihar Kogi ke can kasan teburi.
Yanzu dai kasar nada jimillar mutane 43,537 da suka kamu, 20,087 sun warke sai 883 suka mutu.
