DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBabban Labari ’Yan Nijeriya za su kori APC daga mulki muddin aka gudanar da...

’Yan Nijeriya za su kori APC daga mulki muddin aka gudanar da zaɓen 2027 cikin adalci – Hakeem Baba-Ahmed

Shugaban Jam’iyyar PRP a Nijeriya, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa ’yan Nijeriya za su kada ƙuri’ar korar Jam’iyyar APC daga mulki a zaɓen 2027, muddin aka gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin wata hira da DITV/Alheri Radio a Kaduna, inda ya tattauna kan sauye-sauyen siyasa da dabarun jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Ya ce babban abin da ya kamata APC ta fi tsoro ba jam’iyyun adawa ba ne, illa ’yan Nijeriya, waɗanda su ne ke da ikon yanke hukuncin wanda zai lashe zaɓe.

Baba-Ahmed ya ce jam’iyyun siyasa ba su kada ƙuri’a, don haka ba su ne ke tantance sakamakon zaɓe ba, sai dai al’umma.

Ya ce idan aka bai wa ’yan Nijeriya damar zaɓar shugabanninsu cikin ’yanci, akwai yiwuwar su sauya gwamnati a zaɓen 2027.

“Abin da suke tsoro shi ne idan aka gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, ’yan Nijeriya ba za su zaɓe su ba,” in ji shi.

Shugaban PRP ya kuma yi kira ga jam’iyyun adawa da kada su haɗa kai kawai da nufin kawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki, ba tare da samun cikakken shirin yadda za su tafiyar da ƙasar ba.

Ya ce akwai wasu ‘yan siyasa da burinsu kawai shi ne cire Tinubu daga mulki, amma daga baya su iya ci gaba da aiwatar da irin manufofin da gwamnatin ke aiwatarwa a yanzu.

Baba-Ahmed ya ce PRP ba za ta goyi bayan wani ɗan siyasa kawai saboda yana da burin zama shugaban ƙasa ba, sai dai idan ta fahimci abin da yake son cimmawa da kuma shirin da yake da shi.

Ya ce duk wani ƙawancen siyasa da PRP za ta goyi baya dole ne ta kasance da ingantaccen tsari na magance matsalolin da suka addabi ƙasar, musamman rashin tsaro, talauci, yunwa da wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta.

Shugaban PRP ya ƙara da cewa jam’iyyar za ta yi nazari sosai kan ƙawancen siyasar da ke kunno kai gabanin zaɓen 2027, domin tantance ko masu ruwa da tsaki suna da kyakkyawar manufa ne ko kuma burinsu na kansu ne.

Ya ce jam’iyyar tana da damar gane bambanci tsakanin yaudara da kuma masu kyakkyawar niyya wajen shiga harkokin siyasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata