Home Addini ‘Yan sanda sun kai samame a gidan gyaran dabi’a na “Malam Niga”...

‘Yan sanda sun kai samame a gidan gyaran dabi’a na “Malam Niga” da ke Kaduna

62
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kai samame a wani gidan gyaran dabi’a da ke Kaduna, inda ta yi awon-gaba da wadanda aka tsare a gidan su 147.

A cikin wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da kai samamen a ranar Asabar, inda ya ce ‘yan sanda sun kai samame a gidan gyaran dabi’a na Malam Niga da ke Rigasa a karamar hukumar Igabi da misalin karfe 8 na safe.

Ya ce gwamna Nasir El Rufa’i ne ya jagoranci kai samamen a gidan da ya hada da maza da mata. DSP Sabo ya ce a ya yin samamen, wasu da aka taras a gidan sun yi korafe-korafe da zarge-zargen cin zarafinsu, ciki kuwa ha da zargin yin lalata da mata daga cikinsu.

“Biyo bayan gano gidan da aka yi, gwamna ya ba da umurnin da a kwashe su a kai su sansanin Alhazai da ke Mando Kaduna son ba su kulawa ta musamman. “Kazalika, ‘yansanda sun kama wani mutum mai suna Dr. Lawal Muduru da aka fi sani da Malam Niga wanda shi ke da cibiyar domin a bincikeshi bisa zarge-zargen.

“Ya ce yanzu haka yana taimakawa da bayanai kan binciken a sashen bincike na rundunar ‘yansandan. ” Kazalika, rundunar ‘yansandan na binciken sahihancin takardun rajistarsa,” inji DSP Sabo.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Janga ya kara nanata kwazonsa na yakar dukkanin ayyukan ta’addanci a jihar. Sai ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba rundunar ‘yansandan goyon baya don ta ci karfin aikata laifuka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply