Home Sabon Labari Yan sanda za su takaita kama masu laifi saboda Corona-Taskar Guibi

Yan sanda za su takaita kama masu laifi saboda Corona-Taskar Guibi

121
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin litinin, ashirin da takwas ga watan Rajab, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Maris na shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Zuwa yanzun akwai masu cutar kwaronabairos talatin a kasar nan, sai biyu da suka warke kuma babu mutum ko daya da ya mutu sakamakon cutar. Haka nan mutanen nan biyar da ake zatton suna da cutar a jihar Nasarawa, gwaji ya nuna ba su da ita. A guda talatin da suke da cutar, akwai goma sha tara a Legas, sai hudu a Abuja, sai biyu a jihar Ogun, sai daya a jihar Oyo, da kuma daya a jihar Ekiti.

2. Sakamakon karuwar cutar a jihar Legas, gwamnatin jihar ta umarci ma’aikata da ke matakin albashi na daya zuwa na goma sha biyu, su dakatar da zuwa aiki, su yi zamansu a gida, sai wadanda ke mataki na goma sha uku zuwa sama ne kawai aka yarda su je aiki tunda su ba yawa gare su ba. Amma an yarda wadanda ke muhimman aiki irin na asibiti da sauransu, su je aiki. Ita ma gwamnatin jihar Kwara ta umarci ma’aikata kada su je wajen aiki, su dinga gudanar da aikin daga gida. Ma’aikatan za su zauna a gida na tsawon mako biyu daga yau litinin. Kuma gwamnatin jihar ta amince da shawarar NAFDAC, ta a samar da kulorakwin don gwadawa a gani ko yana warkar da masu cutar kwaronabairos. A sabbin mutum uku masu cutar, biyu sun taho kasar nan da ita ne, sai daya da ya dauka daga wanda ke da cutar sakamakon cudanya.

3. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya umarci manyan jami’ansa na ‘yan sanda, su tabbatar da jama’a na kiyayewa da dokar nesa-nesa da juna, da hana mutum fiye da hamsin taruwa wuri guda, da kuma hana yawan kama mutane barkatai suna tsare su a ofishin ‘yan sanda. Ya kuma ba da umarni rufe duk wata makaranta ta horas da ‘yan sanda daga manyan makarantunsu, zuwa na sakandare, zuwa na firamare.

4. Ministan lafiya ya ce ya dakatar da ganawar da yake yi kullum da manema labaru, da yake bayani filla-filla a kan inda aka kwana a kan cutar kwaronabairos. Ya ce zai dinga fitar da bayanan ta kafofi daban-daban, amma ba a taron manema labaru ba, don gudun yaduwar cutar a wajen taron.

5. Sojoji sun tarbe wasu fataken kayan abinci da sauransu da suke kai wa ‘yan kungiyar Boko Haram a jihar Barno. Sun kona motocinsu makare da kayan abinci irin su shinkafa da sauransu. Suka damke fataken.

6. Wasu ‘yan bindiga sun kashe dan sanda daya, da ji wa wasu sojoji da farar hula rauni, a wani hari da suka kai a jihar Neja.

7. Sojoji sun kashe ‘yan bindiga su ashirin da shida, a jihar Katsina da jihar Zamfara, da karbe bindigogi guda hudu kirar AK47 a hannunsu.

8. Hukumomin reliwe NRC a takaice, sun janye sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na Kaduna zuwa Abuja, da kuma Abuja zuwa Kaduna, da suka fitar da farko. Sun ce jiragen za su ci gaba da dibar fasinja tare da bincikar lafiyar masu shiga.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Na kuwa so in ga shugabannin wasu kasashe da aka ce kowa ya yi zamansa a gida saboda tsoron yaduwar cutar kwaronabairos, na ta kwantar wa da jama’a hankali cewa duk da suna gida suna kulle, za a kula da ba kowa abinci kyauta da kudin kashewa. Hmmm! Na kuwa so in ga wata sanarwa daga ko ma’aikatar kudin kasar nan ne? Na cewa gwamnati za ta dan tsuke aljihunta saboda faduwar farashin mai.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply