Mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya daura alhakin matsalar tsaron da ke ci gaba da addabar Nijeriya yana mai cewa sun kasa jagorantar jama’ar kasar kan turbar da ta dace.

Sa’ad wanda ya bayyana haka a lokacin wani taron jajantawa da sulhu kan wadanda rikicin jihar Plateau ya rutsa da su, ya ce rashin yafiya tsakanin ‘yan Nijeriya itama ta kara ririta wutar rikici a kasar.
A don haka sarkin Musulmin ya yi kira ga jama’ar kasar su zama masu yafiya da kai zuciya nesa da kuma nuna kaunar juna.
A jawabin sat un da farko, gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya nuna bukatar da ke akwai na jama’a su yi watsi da banbance-banbancen da ke tsakanin su tare da nuna yafiya ga junan su.
