Home Labarai ‘Yan siyasa sun yi watsi da mu in ji al’ummar garin ‘Yanduna

‘Yan siyasa sun yi watsi da mu in ji al’ummar garin ‘Yanduna

688
4

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliyar ruwa a garin ‘Yanduna da ke karamar hukumar Baure a jihar katsina.

Matsalar rashin magudanan ruwa dai ta dade tana ci wa mutanen yankin tuwo a kwarya, inda hakan ta sa kusan duk shekara sai an samu irin wannan iftila’i a wannan yanki na ‘Yanduna.

Sai dai tuni mazauna garin suka fara nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda ‘yan siyasar yankin suka yi watsi da su da nuna halin ko in kula wajen kawo abubuwan da za su amfani yankin.

Hashim Bako wani Magidanci ne da ruwa ya cinye gidansa ya bayyana wa DCL Hausa cewa wannan matsala tana damun su matukar aka ce damina ta kama to ba su da kwanciyar hankali.

A karshe ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kawo masu agajin gaggawa domin kauce wa rushewar gine-gine a yankin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

4 COMMENTS

  1. Yan siyaasa basu da kishin al’ummar da suka zabe su, saboda haka ina baiwa mutane shawara da su daina dogaro dasu a kowane lokaci, ya kamata mu fito da wasu hanyoyi na aikin gayya domin muyi maganin matsalolin da suke damun mu.

  2. Allah Ya yasa gwamnati ta duba ta tausaya wajen kawo agajin gaggawa musamman a irin wannan lokacin da al’umma suka fi bukatar taimako Allah kuma ya takaita ya kare gaba

  3. Allah ubangiji yasa hukumomin da abin yashafa su dauki matakin gaggawa,musamman gyara da Kuma samar da mugudanan ruwa a wuraren da abin yashafa domin kare faruwar hakan anan gaba.

  4. Hakika mutanen yanduna dole mu nuna 6acin ran mu saboda gwamnatin jihar katsina tun daga gwamnatin baya kawo zuwa wadda take mulki yanzu sun mayar da al”ummar wannan gari kawai idan za6e yazo mu za6e su daga nan kuma suyi tafiyarsu sun manta da talakkawa allah kabi mana hakkinmu duk shugavan da bazai yi adalci ba ka fitar dashi daga cikin talakkawan da yake zalunta MACIYA AMANAR KASA KAWAI MACIYA AMANAR AL”UMMA

Leave a Reply