Home Kasashen Ketare ‘Yan takarar shugabancin Nijar 3 sun sake kalubalantar takarar Bazoum

‘Yan takarar shugabancin Nijar 3 sun sake kalubalantar takarar Bazoum

95
0

A ranar Talatar makon nan ne, a dai-dai lokacin da kwanaki kalilan suka rage a je zabukan ‘yan majalisar dokoki da na shugaban kasa a jamhuriyar Nijar, wasu ‘yan takarar shugabancin kasar guda uku(3) sun sake kalubalantar takardun zama dan kasa na Bazoum Mohamed dan takarar jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki.

Wadanda suka ajiye takarda kuwa a gaban kotun kundin tsarin mulkin sune Malam Seyni Omar na jam’iyyar MNSD Nasara da ke cikin gungun kawancen jam’iyyar ta PNDS Tarayya, sai kuma tsohon shugaban kasar mulkin soja janar Salou Djibou na jam’iyyar PJP Dubara sai na ukkunsu Ousmane Idi Ango.

Wadannan ‘yan takara dai na bukatar kotun kundin tsarin mulkin ne da ta ba su karin haske kan sahihanci takardar zaman dan kasa ta malanlm Bazoum Mohamed.

Wannan bukatar dai na zuwa ne duk kuwa da cewa kotun kundin tsarin mulkin ta yi kashedi ga ‘yan siyasar da wasu ‘yan kungiyoyin farar hula kan irin kalaman da suke furtawa akan ta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply