Home Kasashen Ketare ‘Yan wasan Man City 2 sun harbu da corona

‘Yan wasan Man City 2 sun harbu da corona

123
0

‘Yan wasan tawagar kungiyar Manchester City biyu Kyle Walker da Gabriel Jesus sun kamu da cutar corona, bayan yi masu gwaji, kamar yadda kulob din ya sanar a ranar Juma’a.

Mai tsaron baya Walker da dan wasan gaba Jesus ba za su buga wasannin Premier League da City’n za ta yi da Newcastle, Everton da Chelsea ba, sai dai akwai yiwuwar za su dawo a wasan da City za ta kara da United a wasan kusa da karshe na kofin Carabao Cup da Manchester United a ranar 6 ga Janairu.

Kazalika kungiyar ta bayyana cewa karin wasu ma’aikatan a kungiyar sun kamu da cutar duk da cewa bata bayyana sunayensu ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply