Home Labarai ‘Yanbindiga sun saci amarya da wata uwa mai shayarwa a Sokoto

‘Yanbindiga sun saci amarya da wata uwa mai shayarwa a Sokoto

123
0

‘Yanbindiga sun sace amarya da wata uwa mai shayarwa a kauyen Sutti da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar “Daily Trust” cewa an sace amaryar ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kai ta dakin mijinta a ranar Laraba 19, ga wannan wata na Agusta.

Majiyar ta ce, uwar da ke shayarwa, mata ce ga Magajin Garin Sulle, inda suka sace ta tare da jaririnta a daren Alhamis.

Majiyar ta ce ‘yanbindigar sun kuma yi awon-gana da wasu ‘yan kasuwa da ba a kai ga tantance yawansu ba akan hanyar su ta Balle zuwa Tangaza a ranar Laraba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply