Home Labarai ‘Yanbindiga sun yi awon-gaba da jami’an tsaro a Kaduna

‘Yanbindiga sun yi awon-gaba da jami’an tsaro a Kaduna

271
0

Masu garkuwa da mutane sun sace wani jami’in hukumar tsaro ta NSCDC (civil defence) da kuma wani dansanda a jihar Kaduna.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa jaridar Muryar ‘Yanci cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren ranar Alhamis a garin Marabar Rido da ke cikin Kaduna.

Kazalika, shaidar ya bayyana cewa ‘yanbindigar da su ka sace jami’an tsaron sun sake kai farmaki gidan Mista Elijah Dreams, shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa. Mista Dreams ya bayyana cewa ‘yanbindigar sun yi awon-gaba da karin wasu mutane biyu da suka hada da wata matashiya.

Ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun bude wa gidansa wuta domin samun damar karya kofar gidan, amma duk da haka ba su samu nasarar shiga gidan ba.

Ya bayyana takaicinsa a kan yadda al’amarin garkuwa da mutane ke kara yawa a yankin, lamarin, da ya sa mazauna yankin ke zaune cikin tsoro da fargaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply