Home Labarai Ƴanbindiga sun yi gargaɗin kai hari lokacin Kirsimeti a Lagos

Ƴanbindiga sun yi gargaɗin kai hari lokacin Kirsimeti a Lagos

123
0

Masu gidaje da al’ummar yankin Dejuwogbo, Oke-Ota Ona da Ikorodu a jihar Lagos sun gudu sun bar gidajensu sakamakon gargaɗin da ƴanbindiga suka bayar na kawo hari a yankin.

Ƴanbindigar sun bada sanarwar cewa za su kawo harin a kwanaki 3 yayin shagalin bikin kirsimeti a yankin tare da neman hadin kan al’ummar don kaucewa zubar jini.

Wadanda ba su tashi sun bar muhallin nasu ba suna cikin dar-dar na yanayin da suka tsinci kansu.

Mutanen yankin sun tashi wayewar garin ranar Asabar suka ga an lika takardar sanarwar a wurare daban daban cikin yankin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply