Home Kasashen Ketare ‘Yancin ‘yan jaridu na fuskantar koma baya a Nijar

‘Yancin ‘yan jaridu na fuskantar koma baya a Nijar

114
0

Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa da kasa Reporters Sans Frontières ta yi Allah wadai da kame-kamen da ake na ‘yan jaridu a Nijar a baya-bayan nan da ta ce zai haifar ma kasar da koma baya a ci gaban da ta yi na ba da ‘yancin ‘yan jaridu a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan.

A kwanakin nan dai a tsakanin wata guda an kama ‘yan jaridu biyu a kasar da suka hada da Ali Soumana shugaban jaridar Le Courrier da aka tsare har tsawon kwanaki biyu a ofishin ‘yan sanda sakamakon tuhumar da ake mishi ta rubuta labarin karya da kuma aka yi ta yada shi a shafukan sada zumunta na zamani kafin daga bisani aka sake shi.

Sai a daya bangare ‘yar jaridar nan Samira Sabou da ake tsare da ita a gidan yarin birnin Yamai tun bayan kama ta da aka yi a ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata sakamakon ita ma tuhumar ta da ake wallafa labarin karya akan dan shugaban kasa a game da badakalar ma’akatar tsaron kasar.

Kungiyar ‘yan jaridu dai ta kasa da kasa ta bukaci a dakatar da tuhumar da ake ma Ali Soumana da kuma gaggauta sakin Samira Sabou da a yanzu haka ke jiran ranar 28 ga wannan wata dan sanin makomar ta bayan masu shigar da kara sun bukaci a rufecta na tsawan mako 5 da biyan tarar miliyan 1 na CFA.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply