Home Sabon Labari YANKIN FUNTUA: SANATA MANDIYA MUN GAJI DA GANI A MAKWABTA-ABDUL DANJA

YANKIN FUNTUA: SANATA MANDIYA MUN GAJI DA GANI A MAKWABTA-ABDUL DANJA

82
0

 

Abdulrahaman Haruna Danja wanda aka fi sani da Abdul Danja matashin dan siyasa ne kuma mai fafutukar ci gaban al’umma. Abin da ke cikin wannan rubutu ra’ayinsa ne ba ra’ayin jaridar DCL Hausa ba.

 

 

Nayi amfani da wannan kalmar ne bawai don wani abu ba sai dai don karin maganar nan na Hausawa da suke cewa ‘a rabe da Guzuma a harbi  karsana’ to anan Sanata Babba Kaita ne karsane mu kuma namu Sanatan ya zama Guzuma!

 

Wai aka ce wata miyar sai dai a makwabta mu dai kam Allah ya jarabcemu na farko tin kafin zuwan Babba Kaita a Matsayin Sanatan Katsina ta Arewa Yan Funtua suke ta fama da kalubale na ayyukan gina al’uma musamman a bangaren dalibai da ilimi da samar ma matasa aikinyi lokacin Abu Ibrahim Yana Sanatan mu!

 

Kafin 2019 mu kai ta rubuce rubuce da sauran matasa irina muna kalubalantar wakilcin Sanata Abu Ibrahim kwatsam sai Allah Ya sake jarabtarmu inji Hausawa su kace ‘wai!’

 

GARA JIYA DA YAU

 

Domin muna ji muna gani na farko bamu da wakilci mai kyau! Duk da Sanatan mu Bello Mandiya yana daya daga cikin Sanatoci wanda suka jagoranci yakin neman zaben Sanata Ahmad Lawan matsayina Shugaban Majalissar Dattawa wato (Senate President) kuma ya samu nasara duk da hakan a banza wai sakarai ya cema wawa wofi!

 

Domin kuwa wannan bai amfani al’umar  Katsina  ta Kudu wato (Funtua Senatorial District) da komai ba, muna ji muna gani yadda sauran Sanatoci suke kankajere wajen samar ma matasansu matsuguni da aikinyi a Gwamnatin Tarayya amman mu ko oho ba a dade ba Sanatan ya samarma wani aiki daga nan Funtua Zone aiki  akai ta cece-kuce wanda su ‘yan Daura zone ‘yan mazabar Babba Kaita su kai ta mana shagube da kuma kalubalantar shi Sanatan nasu cewa donmi zai samarma matasan Funtua Zone aiki!

Sanata Bello Mandiya

Funtua Zone  an riga an barmu abaya kwanan nan Sanatan da Sauran wakilai na Mazabar Daura su kai ta fafutuka akan samar da Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Daura wadda yanzu haka ta tabbata kwatsam jiya sai ga Sanatan na Daura yayi rubutu a shafinsa na sada zumunta wato Facebook cewa

“Federal Polytechnic of science and Technology Daura ta tabbata sauran Federal college of Fire service Kankia loading!”

Wannan idan ka kalli Mazabar Funtua Zone ta Sanata da take da Kananan Hukumomi 11 sai ka yi kuka na bakin-ciki bayan rashin samar ma dalibanmu schoolarship da kuma tallafin karatu da rashin samarmasu aikinyi a guraben aiki sai kaga kuma yanzun babu wata makaranta wacce take mai bada Degree wacce zata taimaki yankin a ilmance!

Mai girma Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari ya kawo NATIONAL OPEN UNIVERSITY OF NIGERIA STUDY CENTER KAFUR, amman duk da haka ‘yan siyasarmu da wakilanmu sun kasa gane yadda za su kawo hanyar da zasu taimaki matasan mu su sami gurbin karatu a wannan jamia ta Kafur, Misali ita Open University samun admission nata na gurbin Degree baya bukatar jamb, ko ace an tafi yajin-aiki yayin aiki kamar yadda sauran jami’o’i  suke zuwa idan kafara sai ka gama. Idan da yan siyasarmu suna da dabara kamar irin shi Sanata Bello Mandiya sai ya tallafi matasa masu karamin-karfi suyi karatu domin muyi gogayya da sauran yankuna na jahar Katsina amman abin shiru kake ji hakan yasa bama kowa bane ya san an kawo Study Center a Kafur ba!

 

Ba kowa bane ya san Open Universitin tana bayar da shaidar digiri ba don haka nan da shekaru masu dama matasanmu anata barin mu a baya!

Duk wani mai kishin yankinsa zai so yaga wakilinshi yana wakiltarshi kamar yadda sauran wakilai suke amman kash! Sai dai muyi ta kishi ana mana kwalele da gwalo muna ta kwadayi amman wakilanmu suna nuna halin ko-in-kula da bukatun wadanda za su zo su taimaki ci gaban yankinsu a siyasance!

Ilimi, aikinyi da samar da sano’i sune abubuwa mafi kyau wanda za su taimaki rayuwar al’uma ta rike kanta da kanta. Ya zama wajibi muyi ta fadakar da wakilanmu da hankaltardasu abin da muke bukata wanda zai taimaki matasa da yankin Funtua Zone bakidaya.

Lokaci yayi da Sanatanmu Bello Mandiya da sauran wwakilanmu na Funtua Zone a matakin Majalissar Wakilai ta Tarayya da Majalissar Dokoki ta jaha dasu tashi tsaye domin muma mu dage ayi tsere damu a kokowar samar da ilimi da aikinyi ga matasa

Bello Mandiya da Rep’s namu muna son muji kunyi maganar Federal University of Agriculture Funtua kowa ya san yankin Funtua da noma da kiwo kusan a cikin Kashi 100% Kashi 99% na mutanend a suke Kananan Hukumomi11 a Funtua Zone manoma ne na rani da damina. Matasanmu suna mallakar Milyoyin kudi a noman rani akan tumatur da kabeji da albasa da sauransu.  Matasan mu ba ragwage bane manoma ne wadanda  basa jiran gwamnati ko aikin gwamnati. Idan ka kalli ma’auni na tattalin arizikin jahar Katsina kasuwannimu suna daya daga cikin kasuwanni mafi rinjaye fitar da hatsi a rani da damina shin mi yasa wakilanmu ba zasu kokari wajen neman mana University of Agriculture ba?

Mun chanchanta yana da kyau wakilanmu su tashi domin irin abin da Sanata Babba Kaita yake ma Daura ya zama izina garesu sun sani muma muna bukata kuma muna kishin yazo garemu!

Wani zai ce qila nayi sauri ki banyi uzuri ba to ga amsa miyasa ssauran wajaje ake yi? Babu uzuri ga shugaban da yaroki al’uma su zabe shi domin ya rike amanar su ko wakilcinsu. Akwai wakilai a matakin Majalissar Dokoki da suke tabukawa irinsu Babangida Talau na Malumfashi/Kafur Allah Ya basu ikon ci gaba dayi. Amman lallai kam shi ma ya hada hannu da Sanata Bello Mandiyya muna bukatar Federal University  Of Agriculture ko a Funtua ko Malumfashi!

Wasu za suce ai ba’a yin Federal University 2 a jaha daya ba gaskiya bane anayi domin wannan ta harkar noma ce muke bukata (agriculture).

 

Amb Abdulrahaman Haruna Danja ya rubuto wa Edita. Za’a iya samunsa a abduldanjah88@gmail.com

Ku aiko mana wasikunku da sharhi akan muhimman al’amuran rayuwa a adireshinmu na email: info@dclmedia24.com

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply