Ministan da ke kula da harkokin ‘yansanda Alhaji Maigari Dingyadi ya ce jami’an ‘yansanda 55,235 aka yi wa karin girma a mukamai daban-daban cikin shekara daya.
Ministan ya bayyana haka ne ya yin jawabinsa dangane da cikarsa shekara guda da fara jagorantar ma’aikatar.
Alhaji Maigari Dingyadi ya kara da cewa jami’an ‘yansanda fiye da dubu 28 ne wadanda ke da mukamin Sergeant da kuma 690 masu mukamin kofur, da kuma fiye da dubu 26 masu mukamin inspector suka samu wannan karin girma.
