Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar bindige wani dan fashi da makami a kan hanyar Bakori zuwa Kabomo, karamar hukumar Bakori jihar Katsina.
A wata takarda daga mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Gambo Isah, ta ce ‘yansandan sun samu rahoton ‘yan fashi sun tare hanyar da misalin karfe 8:30 na daren Talata.
Takardar ta ce babban jami’in ‘yansanda na karamar hukumar Bakori ya jagoranci tawagar ‘yansanda suka isa wurin, aka fara musayar wuta, wanda ta dalilin hakasuka yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan fashin.
Gambo Isah wanda yace ‘yansanda sun kuma yi nasarar kwace bindiga kirar gida, ya ce ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

[…] ‘Yansanda sun bindige dan fashi da makami a Katsina […]