Home Labarai ‘Yansanda sun bindige ‘yan ta’adda a Katsina

‘Yansanda sun bindige ‘yan ta’adda a Katsina

46
0

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina tace ta yi nasarar kashe wasu ‘yan ta’adda 3 tare da kwato bindigu samfurin AK47 guda 2 da alburusai a jihar.

A taron manema labarai a Katsina, kwamishinan ‘yansanda jihar Sanusi Buba yace an kashe ‘yan bindigar ne bayan da suka kai hari a kauyukan Unguwar Bera da Tashar Mangoro a cikin karamar hukumar Dutsinma jihar Katsina.

Yace ‘yansandan Dutsinma sun samu labarin ‘yan bindiga su kusan 50 saman babura sun kai hari a kauyukan biyu a daren Talatar makon nan.

Sanusi Buba yace rundunar ‘yansandan jihar na cigaba da samun nasarar kakkabe ayyukan ta’addanci a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply