Home Labarai ‘Yansanda sun cafke wanda ya fille kan yaro a Bauchi

‘Yansanda sun cafke wanda ya fille kan yaro a Bauchi

129
0

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta ce ta kame Musa Hamza dan shekara 22 bisa laifin yanke kan wani matashi Adamu Ibrahim dan shekara 17 tare da yin gunduwa-gunduwa da shi da nufin yin tsafin kudi a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Wanda ake zargin ya kuma kwakwule idanun mamacin tare da kona kanshi da sauran jikin inda ya rufe su a wani rami da haka.

Mai magana da yawun rundunar’yansandan jihar Mohammed Wakil wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, yace an tono sauran sassan jikin mamacin domin gudanar da gwaji.

Wakil ya shaida cewa yayin tuhumar wanda ake zargin an samu idanun mamacin bayan amsa laifinsa da ya yi ya kuma bayyana cewa wani boka ne ya saka shi aikata hakan don ya samu kudi.

Wakil ya kara da cewa da zarar an kammala bincike za a mika shi gaban kuliya don yanke masa hukunci daidai da laifinsa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply