Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta kama mutane 19 da ake zargi da ta’addanci gami da safarar muggan makamai da garkuwa da mutane a jihar.

An kama bindiga samfurin LAR da harsasai na harbo jirgin yaki 179 da sauran kayan taimakawa a aikata laifi.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Sanusi Buba ya yi takaicin yadda ake samun karuwar yawaitar makamai, lamarin da ya alakanta da iyakoki barkatai da ke da akwai tsakanin jihar da Jamhuriyar Nijar.

Wanda ake zargi da jagorantar tawagar Haruna Yusuf dan shekara 47 da ‘ya’yansa da suka fito daga kauyen Sawarya a karamar hukumar Kaita a cikin jihar Katsina.

Haruna Yusuf lissafto sunayen wasu mutane da yace su ne yake ba makaman idan ya sayo daga wani a kauye a Damagaram Jamhuriyar Nijar, su kuma su kai wa ‘yan ta’adda a a cikin daji.
