Home Kasashen Ketare YANSANDAN CHINA SUN FARA BINCIKEN MUTUWAR WANI DAN NIJERIYA

YANSANDAN CHINA SUN FARA BINCIKEN MUTUWAR WANI DAN NIJERIYA

69
0

Saleem Ashiru Mahuta

Shugaban karamin ofishin jakadancin Nijeriya a Kasar China Wale Oloko a ranar Larabar nan yace jami’an yan sandan kasar Chinan sun fara bincike kan musabbabin mutuwar wani dan Nijeriya Unachukwu Nwajueze.

Oloko yayi wannan bayani a cikin wani sakon Email da ya aike wa kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN a Lagos, yana mai cewa marigayi Nwajueze ya mutu ne a kasuwar Tong Tong da ke Guangzhou A ranar 12 ga watan Agustan da muke ciki.

A cewarsa kananan ma’aikatan jakadancin sun dauki matakin gaggawa na shiga tsakani domin kwantar da hankulan yan Nijeriya kan bukatar da suka nema na sanin musabbabin mutuwar Nwajueze.

Lokacin da Shugaba Buhari ya ziyarci China

Oloko ya kuma bayyana cewar tuni ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai da matar mamacin bisa mutuwar tasa, in da ya hadu da wasu jami’an gwamnatin kasar wanda su ma suka kai ziyarar ta’aziyyar inda suka yi kira ga sauran yan Nijeriya mazauna Birnin Guangzhou dasu kwantar da hankulan su, in da suka bada tabbacin gudanar da bincike dai dai da tsarin kasar ta China.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply