Home Labarai Yanta’adda sun kashe mutane da sace wasu da dama a Kaduna

Yanta’adda sun kashe mutane da sace wasu da dama a Kaduna

39
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kashe mutane 3 a kananan hukumomin Giwa da Zangon Kataf a jiya Litinin.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro sun bada rahoton harin da ƴanta’adda suka kai a kauyen Garawa, Doka da Unguwan Yaya duka a yankin Fatika a karamar hukumar Giwa inda suka kashe mutane 2 tare da sace wasu da yawa.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya shaida cewa ƴanta’addan sun kai hari wurin shakatawa a kauyen Wawan Rafi a karamar hukumar Zangon Kataf inda suka kashe mutum daya tare da jikkata 3.

Ya kuma shaida cewa jami’an tsaro sun samu bindiga kirar AK47 guda 2 tare da katan 43 na alburushi a wurin wasu mutane 2 da aka kama kuma.

Ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufa’I ya bayyana bakin cikinsa kan lamarin ya kuma yi addu’a ga mamatan tare da jajanta abin da ya faru a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply