Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi maraba da sabon rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS), wanda ya nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya samu ci gaban kashi 4.43 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2026, daga kashi 4.23 cikin 100 da aka samu a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.
Mai ba shugaban shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya ruwaito rahoton ya nuna cewa bangarorin noma, masana’antu, man fetur da iskar gas, da kuma ayyukan yi sun samu ci gaba.
Bangaren kwadago ya ci gaba da kasancewa mafi girman mai bayar da gudunmawa ga jimillar GDP, yayin da jimillar GDP din kasar a rubu’i na biyu ya kai naira tiriliyan 119.27, daga naira tiriliyan 100.7 a shekarar da ta gabata.
Tinubu ya ce rahoton ya zo a lokacin da ya dace, musamman ganin yadda jam’iyyun adawa ke kokarin rage darajar nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Ya ce gwamnatin ta dauki matakai masu tsauri cikin shekaru uku domin daidaita tattalin arzikin kasar da kuma kafa tubalin ci gaba mai dorewa ga ƙasar.
Shugaban ya bayyana cewa sakamakon gyare-gyaren na kara fitowa fili, inda ya ambaci samun rarar cinikayya, karuwar ajiyar kudaden waje zuwa matakin da ya fi na shekaru 17, da kuma ingantuwar matsayin Nijeriya wajen tantance cancantar samun lamuni daga ketare.
Ya kuma ce samar da man fetur da iskar gas na karuwa, yayin da masu zuba jari da suka bar kasar ke fara dawowa sandiyyar fara daidaituwar al’amura.
Tinubu ya ce gwamnati na ci gaba da gina manyan ayyukan more rayuwa, ciki har da tituna, layukan dogo da manyan hanyoyin mota. Ya kuma bayyana cewa jami’o’in Najeriya sun samu kwanciyar hankali daga yajin aikin da aka dade ana fuskanta, yayin da shirin rancen karatu na NELFUND da kuma tallafin bashi ta Creditcorp ke taimakawa wajen rage wa jama’a nauyin samun ilimi da kudi.
Ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki wasu matakai cikin makonni masu zuwa domin rage radadin da al’ummar da ke cikin mawuyacin hali ke fuskanta.
Matakan da ya ce sun hada da samar da sufuri mai rahusa, kara samar da abinci da kuma aiwatar da shirye-shiryen tallafi da za su kai ga jama’a a matakin kasa-kasa.
Tinubu ya ce tattalin arzikin Nijeriya yana kan hanyar samun karin ci gaba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta mayar da hankali wajen ganin ci gaban tattalin arzikin ya koma ingantacciyar rayuwa ga ’yan kasa.
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta huta ba wajen tabbatar da dorewar nasarorin da aka samu da kuma ganin jama’a sun fara jin tasirin su a gidajensu da aljihunsu.
