Rahotanni sun nuna cewa shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari na gudanar da taro a halin yanzu tare da gwamnonin ƙasar.
Ana dai gudanar da taron ne ta hanyar tangaraho, inda shugaba Buhari ke halartar sa daga fadar sa da ke Abuja.
Ba a bayyana abubuwan da taron ya ƙunsa ba, amma dai bai rasa nasaba da Covid-19.
Daga cikin masu halartar taron tare da Buhari akwai Ministar kuɗi, Ministan shari’a da gwamnan babban bankin Nijeriya CBN kamar yadda hoton da fadar shugaban ƙasar ta fitar ya nuna.
A gefe guda kuma, shugaban ƙungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Ekiti Dr Kayode Fayemi ne ke jagorantar gwamnonin a wajen taron.
