Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya janye dokar hana fita a ƙananan hukumomin Safana da Mani.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa ya fitar ta ce an ɗauki wannan matakin ne saboda ba a samu ɓullar cutar Covid-19 ba a cikin mako biyu a ƙananan hukumomin sannan waɗanda suka kamu suma sun warke.
Gwamnan ya roƙi jama’ar ƙananan hukumomin da sauran jama’a su ci gaba da tsare ƙa’idojin kare kai daga kamuwa da cutar.
A ranakun 23 da 25 ne dai ga wata Afirilu aka sanar da rufe ƙananan hukumomin Safana da Mani, bayan an samu wasu da suk kamu da cutar.
