Home Labarai Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Jihar Kaduna ya yi murabus.

Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Jihar Kaduna ya yi murabus.

76
0

Ahmadu Rabe
Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Alhaji Aminu Shagali ya yi murabus.

Murabus din na shi ya zo ne a dai-dai lokacin da wasu daga cikin mambobin majalisar ke shirin tsige shi daga kujerar ta shi.

Tanimu Musa wanda dan majalisa ne a jihar kuma shi ne ya ke jagorantar kwamitin yada labarai , yace kakakin majalisa “ya sanar da murabus din nasa ranar Talata.

Tanimu ya kara da cewa yanzun tsohon kakakin majalisa jahar zai ci gaba da zama a matsayin sa na dan majalissa kamar sauran mambobi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply