Home Labarai ‘Yar fim na murnar cika shekaru 2 ba tare da yin jima’i...

‘Yar fim na murnar cika shekaru 2 ba tare da yin jima’i ba

83
0

Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayo ta Nollywood Uche Ogbodo tace rayuwarta ta yi matukar sauyawa saboda ta daina yin jima’i.

DCL Hausa ta samu labarin cewa ‘yar kimanin shekaru 34, Uche da ke zawarci da danta daya, ta yabi kanta da cewa ta yi mamakin yadda ta kwashe shekaru biyu cur ba tare da yin jima’i ba. Ta kara da cewa har kumari ma tafi a halin yanzu kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Uche Ogbolo da ta sanar da hakan ne a shafinta na Instagram, tace tsawon wannan lokacin bata kusanci wani namiji ba. ‘Yar wasan kwaikwayon tace abin ya yi matukar burge ta da ta dauki wannan matakin, kuma jikinta na yin kyau.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply