Home Sabon Labari ‘Yar shekara 13 ta haihu bayan an yi mata fyade a Jigawa

‘Yar shekara 13 ta haihu bayan an yi mata fyade a Jigawa

862
0

Kungiyar kare hakkin dan adam mai suna π‚π’π­π’π³πžπ§π¬ π”π§π’π­πžπ 𝐟𝐨𝐫 𝐏𝐞𝐚𝐜𝐞 𝐚𝐧𝐝 π’π­πšπ›π’π₯𝐒𝐭𝐲 (CUPS) ta ce tana cigiyar wani matashi mai suna Idiyo dan a kauyen KETAKO, AUDALLAWA a yankin Kafin Hausa na jihar Jigawan Nijeriya. Kungiyar ta yi zargin cewa matashi Idiyo ya yi wa wata yarinya mai shekaru 13 fyade kuma ta haihu a makon da ya gabata bayan ta yi fama da nakuda mai tsanani.

Dakta Idris Ahmed Shugaban Kungiyar CUPS

Shugaban kungiyar ta CUPS Dakta Idris Ahmed ya ce bayanan da suka samu sun ce matashin da ya yi wa yarinyar wannan aika-aika bai shiga hannun hukuma ba a saboda abin da ya kira gazawa ta ‘yan sandan Nijeriya.

A yanzu kungiyar CUPS neman bayanan da za taΒ  tunkari kotu da su don ganin an kamo Idiyo wanda rahotanni ke cewa ya musanta cewa shi ya yi wa yarinyar fyade har ta samu ciki ta haihu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply