Home Labarai Yara sama da milyan 2.5 ne ke fama da tamowa a Nijeriya...

Yara sama da milyan 2.5 ne ke fama da tamowa a Nijeriya – Minista

109
0

Gwamnatin Nijeriya ta ce akwai yara ‘yan kasa da shekaru 5 sama da milyan 2.5 da ke fama da karancin abinci mai gina jiki da ya haddasa musu tamowa.

Karamin ministan kasafin kudi Clem Agba ne ya sanar da hakan a lokacin bikin kaddamar da makon abinci mai gina jiki na 2020 a Abuja.

Ministan yace yawan yaran ya sa Nijeriya ta zamto ta 2 a kasashen duniya da ke fama da matsalar.

Clem ya koka da cewa yanayin abincin kasar da matsalar tattalin arziki ne suka jawo wannan matsala.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply