Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya sanar a shafinsa na Twitter cewa daya daga cikin ‘yayansa ya kamu da Coronavirus.
Atiku ya ce tuni ya sanar da mahukumtan Nijeriya har ma an kwantar da yaron nasa a asibiti.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya bukaci jama’a da su sanya dansa a cikin addu’a a saboda wannan cuta.
Kawo safiyar Litinin din nan akalla mutane 30 ne dai ke dauke da cutar , galibi a jihohin da ke kudancin kasar.
