Home Kasashen Ketare Yau ce ranar zaɓen shugaban ƙasa a Amirka

Yau ce ranar zaɓen shugaban ƙasa a Amirka

83
0

A ranar Talatar nan ne al’ummar ƙasar Amirka za su zaɓi ko waye zai zama Shugaban ƙasa tsakanin shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyyar Republican da kuma Joe Biden na Democrat.

Trump da Biden dai sun kammala yaƙin neman zaɓensu a daren jiya Litinin.

Ya zuwa yanzu dai tuni Amirkawa fiye da milyan 100 suka jefa ƙuri’arsu, sai dai a wannan karon jihohin Arizona, Florida, Georgia, Michigan, Minnesota, North Carolina, Pennsylvania, Wisconsin su ne jihohi 8 da ƴan takarar za su fi son samun ƙuri’u daga nan.

Sai kuma samun ƙuri’u biyu bisa uku na electoral college 538, wato ana son ɗan takara ya samu aƙalla ƙuri’u 270 na electoral college kafin samun damar lashe zaɓen na ƙasar Amirka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply