Hukumar kula da hasken lantarki ta Nijeriya NERC ta amince da karin kudin wutar lantarki daga daya ga watan Satumba, 2020.
Hakan ya zo watanni 3 bayan da majalisar dokoki ta kasa ta hana a yi karin wutar lantarkin duba da yanayin tattalin arzikin da ake fama da shi.
Amma a wasu takardu da jaridar Punch ta gani, sun nuna cewa karin kudin wutar lantarkn zai fara aiki ne daga 1 ga watan Satumba.
