Home Sabon Labari Yemen: Yan tawayen Houthi na neman zaman lafiya da Saudiyya duk da...

Yemen: Yan tawayen Houthi na neman zaman lafiya da Saudiyya duk da harin da aka kai mata

60
0

Yan tawayen Houthi na kasar Yemen masu samun goyon bayan kasar Iran sun ce za su dakatar da kai hare-hare na makami mai linzami ga kasar Saudi Arabia, kamar yadda suka tabbatar a yammacin jumaar nan.

Yan tawayen Houthi sun yi ikirarin cewa sune suka kai hare-hare na baya-bayannan da aka kai a babbar masana’antar sarrafa man fetur ta kasar Saudi Arabia.

Houthi dai suna fatan Riyadh za ta duba wannan lamarin da kyakyawar fahimta. Sun kara da cewa idan har kasar Saudi Arabia basu nuna kyakyawar fahimta akan wannan lamarin ba, su ka ci gaba da jeho masu bamabamai ta sama ,to suna da cikakkiyar damar da za su maida masu martani kamar yadda Mahdi almashat shugaban yan tawayen ya bayyana .

A wata hira da gidan talabijin na Al-masirah suka yi da shi Almashat ,ya yi kira ga mutanan kasashen waje dasu daina cin mutuncin mutanan kasar Yemen, domin basu san irin wahalhalun da suke fuskanta ba .

Al-mashat ya yi kira da ayi gaggawar bude filin jirgin Sana’a, a kuma daina tarbe jiragen ruwansu masu zuwa tashar jirgin ruwa ta Hodeida .

Shugabannin yan tawayen Houthi sun ce ci gaba da yakin ba zai haifar da da mai ido ba ga dukkan bangarorin, kuma idan aka daina yakin zai kawo gagarumin cigaba a yankunan .

Da dai sanyin safiyar juma’a kawayen kasar Saudi Arabia masu goya mata baya don yakar yantawayen Houthi suka ce sun kai wasu hare-hare ga yan tawayen ta sararin samaniya .

Mai magana da yawon kawayen kasar Saudi Arabia, Turki al-maliki ,yace kasashen da ke kawance da Saudi Arabia sunkai hari mai zafi ga yantawayen Houthi, inda sukafi maida hankali a arewacin lardin Hodeida dake yammacin kasar Yemen, kamar yadda kafar yada labarai ta Saudiya ta ruwaito.

Mai magana da yawun yantawayen Muhammad Abdulsalam yayi kira da cewa mummunan hare-haren da ake kaiwa yawuce misali Wanda yajawo lalacewar shirin yarjejeniyar tsagaita wuta Wanda majalisar dinkin duniya tasa baki a watan Disamba da ya gabata a kasar Sweden.

Tashin hankali dai ya karu tun karshen mako da aka kai hari ga masana’antar sarrafa man fetur ta kasar Saudi Arabia.

Kasar Saudi Arabia da kasar Amuruka dai sun dora alhakin hare-haren da aka kai ga kasar Iran,amma Tehran ta musanta zargin .

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply