Home Labarai Yunkurin samar da karin iskar gas a Nijeriya

Yunkurin samar da karin iskar gas a Nijeriya

112
0

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da wani shiri kan yadda za a rika sufuri da kuma zirga-zirgar iskar gas a kasar domin ci gaba da bunkasa kasuwar iskar gas.

Karamin Minista a ma’aikatar man fetur Timipre Sylva ya sanar da hakan a ya yin da ya ke kaddamar da shirin fasahar zamani akan yadda ake samar da iskar gas da aka gabatar a Abuja.

Ministan ya kara da cewa tuni wannan gwamnatin ta samar da sabbin tsare-tsare wajen kawo ci gaba a harkar samar da iskar gas da kuma sabbin hanyoyin da za su taimaka wa ayyukan cikin gida da ma na kasashen waje.

Timipre Sylva ya kara da cewa manufar yin hakan dai ita ce domin a fadada samar da iskar gas a cikin gida Nijeriya da kuma magance kalubalen da tiririn iskar gas din ke haifar wa, a wajen da ake samar da shi.

A karshe ya kara da cewa gwamnati ta samar da wasu shirye shirye guda uku akan sha’anin iskar gas domin kara bunkasa bangaren da yake samar da shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply