Hannatu Mani Abu
Gwamnatin tarayyar Nijeriya za ta gina famfunan tuka-tuka dari biyu da casa’in(295) tare da wurin bahaya dari da hamsin da biyu (152) a kananan hukumomi bakwai (7) da rikice-rikece ya shafa a jihar Adamawa.
Dr. Maurice Vonubolki jagoran aikin gyare-gyaren wuraren da rikicin ya shafa ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labaru na Nijeriya NAN hakan a birnin Yola.
Vonubolki ya ce shirin hadin gwiwa ne da gwamnatin tarayya da kuma bankin duniya domin gyara da kuma gina sabbin ababen more rayuwa da aka lalata sakamakon hare-haren da aka kai a yankunan.
Ya ce za a gudanar da gyaran ne a jihohi uku da suka hada da Adamawa da Borno da kuma Yobe.
Yanzu haka dai an riga an yi famfunan tuka-tuka guda 295 da wasu famfunan guda 50 masu amfani da hasken rana.
Haka kuma an gina wuraren bahaya guda 152 a kananan hukumomi bakwai da hare haren ya shafa.
Wuraren da suka amfana sun hada da Madagali da Maiha da Hong da kuma karamar hukumar Gombi.
